Connect with us

News

NYSC Ta Mayar Da Martani Game Da Kama Wani Dan Bautar Kasa

Published

on

NYSC

Daga Khadija Abdullahi Mahmud 

 

 

 

Hukumar masu yiwa kasa hidima ta kasa (NYSC) ta yi Allah-wadai da wani magudin zabe da ake zargin wani jami’in hukumar, Orji Nkenna da wasu ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a jihar Osun suka yi.

Jerin Tafiye-Tafiyen Da Buhari Ya Yi Zuwa Ketare A Bana

Advertisement

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC, Mista Eddy Megwa, ya fitar ranar Lahadin nan a Abuja.

 

A cewarsa, abin takaici ne a ce Nkenna, wanda yana daya daga cikin wadanda ake tuhuma, zai iya kaskantar da kansa cikin irin wannan danyen aikin.

 

“Mun kuma lura cewa ana gudanar da bincike a kan lamarin, kuma idan aka same shi da laifi a bi doka yadda ya kamata.

 

Advertisement

“Hukumar NYSC, a matsayinta na kungiyar gyare-gyaren matasa, don haka ta nisanta kanta daga irin wannan rashin kishin kasa na masu laifi,” in ji shi.

Ya kuma ce dukkan ‘yan hukumar, tun daga sansanonin wayar da kan jama’a, a kullum jami’an NYSC da na INEC suna wayar da kan su kan irin rawar da suke takawa a lokacin zabe, ciki har da takunkumin da aka kakabawa mata, idan har suka saba wa dokokin zabe.

“Saboda haka, duk wani jami’in kungiyar da ya tsunduma kansa a kowane irin laifi na zabe, dole ne ya fuskanci fushin doka, kamar yadda dokar zabe ta tanada.

 

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Osun a ranar Asabar din nan ta ce ta kama Nkenna, da wani jami’in hukumar zabe ta kasa INEC da kuma wani da ke da alhakin kula da katunan zabe na dindindin (PVCs).

 

Advertisement

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Yemisi Opalola, ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar da sauran su, sun yi amfani da katin zabe a ofishin tattara kudaden karamar hukumar su, da ke karamar hukumar Atakumosa ta Yamma. (NAN)

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending