Connect with us

News

YAN BINDIGA SUN KUTSA KAI HAR CIKIN GIDA SUN SACE WANI BASARAKE A ABUJA

Published

on

DAGA KHADIJA ABDULLAH MUHMD 

 

 

 

 

Yan bindiga sun kutsa kai har cikin gidan wani Hakimi a Abuja, sun yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da har yanzun ba’a gano ba

Advertisement

Wani shugaban al’umma a yankin da abun ya faru ya ce maharan sun shafe kusan awa ɗaya amma babu wanda ya kawo ɗauki

Kwamandan rundunar yan sanda na yankin Kubwa, ACP Muhammad Ndagi, ya ce sun fara bincike kan lamarin tun tuni

Mun mayar da kamfanin NNPC hannun ‘yan kasuwa – Buhari

Wani shugaba a yankin, wanda ya zanta da Daily Trust, ya ce an sace Malam Isiyaka Dauda a cikin gidansa, wanda ke nesa da fadarsa yayin harin yan bindiga.

 

Ya ce yan bindiga kusan su 10 sun buɗe wuta sau biyu suna dira gidan, hakan ya ankarar da Yan sa’kai, inda ya ƙara da cewa tilas yan Sa’aki suka yi takansu yayin da masu garkuwan suka nufe su.

Advertisement

A cewarsa maharan sun kutsa kai ta tsiya cikin wani ɗaki da ke cikin gidan, kafin daga bisani suka sake fasa wani ɗakin wanda suka samu Basaraken a ciki.

“Sun yi awon gaba da shi ba tare da fuskantar wata tirjiya ba, kuma sun bi ta hanyar da zata kai mutum garin Bwari,” a cewar mutumin.

Har zuwa jiya Litinin da yamma, babu wani rahoton da ke nuna cewa masu garkuwan sun tuntuɓi wani daga cikin iyalansa ko a yankin.

Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka?

Kwamandan rundunar ‘yan sanda na yankin Kubwa, mataimakin kwamishinan yan sanda ACP Muhammad Ndagi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yanzu haka jami’ai na kan bincike.

 

Advertisement

 

SOURCE DAILY TRUST

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending