News
An ba da belin ƴar fafutukar da ake tuhuma kan rikicin da aka yi a Indiya tun 2002
DAGA MARYAM BASHOR MUSA
Hukumomi a Indiya sun saki wata fitacciyar ‘yar fafutuka da aka ɗaure a gidan yarin Gujarat, kwana guda bayan kotun ƙolin ƙasar ta bayar da belinta.
An kama Teesta Setalvad sama da wata biyu baya, bisa zargin gabatar da wasu takardun karya kan wata zanga-zangar addini da aka yi shekaru 20 baya.
A yayin zanga-zangar, an kashe sama da mutum dubu wadanda mafi yawancinsu musulmai ne.
Lokacin da abin ya faru, Firaministan Indiya na yanzu Narendra Modi, na matsayin ministan cikin gida, kuma ta riƙa zarginsa da hannu cikin rikicin, abin da magoya bayansa suka musanta.
BBC NEWS
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
