News
Nasa ta sake soke ƙudirin harba gagarumin kumbo zuwa duniyar wata karo na biyu cikin mako ɗaya
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, Nasa ta soke shirinta na Artemis na harba wani gagarumin kumbo zuwa duniyar wata, karo na biyu a cikin ‘yan kwanaki.
An ɗage shirin harba kumbon ne, wanda shi ne mafi girma da aka taba ƙerawa bayan da aka gano yana yoyon mai.
Ƴan Sanda sun kama matar da ta shirya aka yi garkuwa da mijinta
Ƙwararru a Cibiyar Sararin Samaniya ta Kennedy sun kasa warware matsalar. An gano yoyon ne bayan da aka zubawa tankokin kumbon man hydrogen.
Error: Contact form not found.
Babu kowa a cikin katoton kumbon, amma burin shirin na Artemis shi ne sake tura ƴan adam zuwa duniyar wata a shekarar 2025.
A ranar Litinin din da ta gabata ne aka soke aika kumbon daga ranar farko da aka so yin hakan saboda matsalar na’ura. Akwai damar sake gwada harba shi a jibi Litinin ko Talata.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
