Connect with us

News

Obasanjo Yace Ya Yi Nadamar Goyon Bayan Buhari A 2015

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

 

 

 

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce ya yi nadamar goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari a shekara ta 2015.

Advertisement

Obasanjo ya bayyana haka ne, yayin hirar sa da wata marubuciya Ifedayo Agoro a jirgin sama, wadda ta wallafa a shafin ta na Twitter, inda ta ce ta hadu da Obasanjo a baya-bayan nan kuma ta zauna kusa da shi a jirgin sama.

Yadda Ta Kaya A Manyan Wasannin Firimiyar Ingila Ranar Asabar

Miss Agoro Ta ambato Obasanjon ya na cewa, na yi babban kuskure wajen goyon bayan shugaba Buhari, domin bai san komai game da tattalin arziki ba.

Obasanjo, ya ce babban kuskuren da su ka yi shi ne, sun yi tunanin shugaba Buhari zai yi yaki da cin hanci da rashawa da rashin tsaro, sannan ya zabi mutanen da su ka san tattalin arziki da ayyuka.

Tsohon shugaban kasar, ya kuma zargi matasan Nijeriya da rashin hadin kai wajen yakar tsofaffin ‘yan siyasa, ya na mai cewa, idan matasa ba su tashi da gaske sun canza shugabancin Nijeriya ba babu abin da zai sauya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending