News
Yajin Aikin ASUU: NANS Tayi Barazanar Rufe Filayen Jiragen Sama Najeriya da ga gobe litini
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN
Kungiyar ta ce zata dauki wannan mataki ne domin jawo hankalin gwamnati kan yakin aikin da ya shiga wata na bakwai
Biyo bayan takun saka tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU na tsawon watanni bakwai, kungiyar dalibai ta kasa NANS ta bayyana aniyar ta na dakatar da aiki a dukkan filayen jiragen sama na kasa da kasa.
Sojojin Sama Sun Yi Luguden Wuta A Sansanin Gogarman Yan Bindiga Bello Turji
Kungiyar NANS ta kasa ta yi taro a karshen mako a Akure, babban birnin jihar Ondo, inda ta yi Allah-wadai da yadda gwamnatin tarayya ke mu’amala da malaman da suke yajin aiki da kuma ilimi gaba daya.
Daliban sun yi ikirarin cewa an yi nasarar rufe manyan tituna na tsawon kwanaki hudu, dalilin da ya sa suka yanke shawarar dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasashen waje daga ranar 19 ga Satumba, 2022, domin jawo hankalin gwamnati.
Mun rawaito cewa daliban zasu yi wannan aiki ne domin mahukunta su fuskanci wahalar da daliban suka sha na watanni bakwai da suka gabata.
Shugaban Hukumar NANS na “Karshen Yajin aikin ASUU Yanzu”, Ojo Raymond Olumide, ya bayyana cewa tuni daliban sun gaji da rokon bangarorin biyu kan wajibcin kawo karshen yajin aikin a yayin wata ganawa da manema labarai.
“Dole ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta warware duk wasu basussukan da ake bin malamai da kuma albashin malamai”, Olumide, ya kara da cewa filayen jiragen saman da za a mamaye za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an janye yajin aikin.
