News
2023: Idan aka zabe ni dan majalisar jaha zan dawo da martabar Dala – SAGIRU U BANDERAWO
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan takarar majalisar jaha na a tutar jam’iyyar ADP SAGIRU U BANDERAWO yace Idan al’ummar karamar hukumar Dala suka zabe shi a zabe mai zuwa zai dawo da martabar dala ta hanyar gudanar da aiyukan cigaba.
SAGIRU U BANDERAWO Wanda ake yiwa lakabi da BANDERAWO ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da wakilin jaridar indaranka a kano
Nafi kowanne dan takarar majalisar jaha a Dala chanchanta-SAGIR U BANDERAWO
Yace dan takarar gwamna Sha’aban Sharada a jam’iyyar ADP yana da tsari yadda zaya gabatar da aiyukan aiyukan Raya Kasa da cigaban al’umma Waɗanda suka hadar da bunkasa Ilimi,Noma da ciwo samar da aiyukan yi ga Matasa ta hanyar bayar da jari ,Lafiya, inganta tsaro, samar da hanyoyi da dai Sauransu.
Da wannan damar zamuyi amfani wajan samarwa da al, ummar karamar hukumar Dala aiyukan cigaban matasa.
Banderawo ya Kuma Kalubalanci Gwamnatin Jihar kano bisa yadda ta yi watsi da muhimman aiyukan cigaba matasa
“Zamu yi gwamnati budadiya wacce zata tafi da kowa , Inda zamu Rika tuntubar masu Ruwa da tsaki a duk Inda buƙatar hakan ta taso” inji Banderawo
Dan takarar ya yaba da yadda jam’iyyar ADP take Samun karbuwa a Kano da duk jihohin kasar nan, Inda ya bayar da tabbacin Idan al’ummar Jihar Kano suka zabi jam’iyyar a 2023 zasu gabatar da kyawawan manufofi n jam’iyyar.
