Connect with us

News

Kotu ta tabbatar da Machina a matsayin halartaccen dan takarar APC na Yobe ta Arewa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Damaturu cikin jihar Yobe ta tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halartaccen dan takarar sanata na jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa.

Advertisement

 

Bashir Sharrif Machina dai tun farko ya ce ba zai sauka ko janyewa kowa takararsa ta majalisar dattijai ba.

Advertisement

Za’ayita Ta ƙare Ahmed Lawan da Bashir Machina

Jam’iyyar APC mai Mulki ce ta miƙa sunan shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Lawan ga hukumar zaɓe a matsayin ɗan takarar sanata mai wakiltar Mazaɓar Yobe ta Arewa maimakon Bashir Machina, wanda ya ci zaɓen fitar da gwani na mazaɓar.

Advertisement

 

Abdullahi Adamu ya yi iƙirarin cewa Sanata Ahmad Lawan ya sayi fom kuma ya shiga zaɓen fitar da gwani na sanatan Yobe ta Arewa, sai dai Bashir Machina ya ce shi kaɗai ya tsaya takara a zaɓen.

Advertisement

 

Tun bayan rashin nasara da ya yi a zaben fitar da gwani na takarar shugaban ƙasa a APC, aka fara takaddama kan makomar siyasar Sanata Ahmad Lawan bayan ya shafe fiye da shekara 20 yana wakiltar al’ummarsa a Majalisar Wakilai da ta Dajjitai.

Advertisement

 

Wannan hukunci na babbar kotun tarayya a ranar Laraba na nufin Ahmad Lawan ya rasa dama ta yiwuwar komawa majalisar dokokin Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending