Connect with us

News

Gwamnatin Kwara Ta Dakatar Da Likitan Da Ake Zargi Da Hallaka Wasu Mata A Jihar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnatin jihar Kwara ta saka Dokta Adio Adebowale, wanda ake zargi da yin garkuwa da wasu mata biyu a jihar kan dakatar da shi har sai baba ta gani.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar ta tabbatar da matsayin Adebowale a matsayin kwararren likita kuma mamba a kungiyar.

Advertisement

Habasha Ta Dakatar Da Bai Wa ’Yan Najeriya Biza A Kasarta

 

Advertisement

Ana zargin Adebowale, babban Darakta na babban asibitin Kaiama da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara, inda ya kashe wasu mata biyu, daya daga cikinsu budurwarsa ce, tare da binne su a wurare daban-daban.

JARIDAR ALKIBLAH ta tattaro a ranar Talata a Ilorin cewa babban kwamitin gudanarwa na ma’aikatar lafiya ta jihar ne ya dakatar da Adebowale, wanda ke da alhakin daukar matakin ladabtarwa ga manyan ma’aikatan hukumar kula da lafiya ta jihar Kwara.

Advertisement

Har ila yau, kwamishinan lafiya na jihar, Dr Raji Razaq, yayin da yake tsokaci kan lamarin ya ce, “Eh, ina tabbatar muku da cewa an dakatar da shi kuma an dakatar da albashinsa har sai an kammala bincike kan ayyukansa wanda hukumomin tsaro suke gudanarwa.

“Ana zarginsa da aikata wani laifi. Dole ne mu dakatar da shi kuma mu dakatar da albashi. Dole ne mu jira wasu ayyuka har sai lokacin da aka kammala bincike, kuma kun san cewa ana ganin mutum ba shi da laifi har sai an tabbatar da shi da laifin da ake zarginsa da shi ta hanyar kotun da ta dace. Za mu jira har sai an kammala bincike sannan kotu ta tabbatar da wanda ake tuhuma da laifi kafin mu dauki wani mataki na daban.”

Advertisement

Da aka tuntubi Shugaban Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Kwara, Dokta Abdulraheem Malik, ya tabbatar da cewa Adebowale mamba ne na hukumar amma ya ce ba zai iya cewa komai kan dakatarwar ba saboda ba da dadewa aka nada shi ba.

Lokacin da aka tambaye shi don yin sharhi game da halin Darakta na Likita, Malik ya ƙi, yana mai cewa bai san halinsa sosai ba.

Advertisement

“Ba zan iya cewa komai da yawa game da shi ba saboda sabo ne a wannan ofishin; Yanzu dai makonni biyu da suka gabata gwamnati ta nada ni,” inji shi.

A halin da ake ciki, shugaban kungiyar NMA reshen jihar Kwara, Dr Abdulkadir Ahmed, ya tabbatar a Ilorin a ranar Talata cewa Adebowale mamba ne a kungiyar kuma yana aiki da gwamnatin jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending