News
KARFE 10 NA SAFIYAR RANAR JUMMA A, A BUHARI ZAI GABATAR DA KASAFI A ZAUREN MAJALISA
DAGA KHADIJA ABDULLAHI MAHMUD
Kakakin Majalisar Dattijai Ahmad Lawal ya tabbatar da cewa Shugaban kasa Muhammad Buhari zai gabatar da kasafin shekarar 2023 dake tafe.
Yayin zaman daya gabata a yau Ahmad Lawal yace zasu karbi bakuncin Buhari ranar Jumaa da misalin karfe 10 na safiya.
Zargin kisan Ummita: Kotu Ta Baiwa Gwamnatin Kano Umarnin Samar Wa Ɗan China Tafinta
Hasashen kasafin da Shugaban zai gabatar ya kai naira tiriliyan 19.76.
Yan majalisar Wakilai zasu hadu a zauren Majalisar Dattijai don tarbar Shugaban da sauraren jawabin karshe na Shugaban kasa Muhammad Buhari.
Advertisements
