News
Shugaba Buhari da Osinbajo zasu kashe naira biliyan 11.92 na abinci da tafiya kasashen waje.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo zasu kashe naira biliyan 11.92 na abinci da tafiye-tafiye hadda na zuwa kasashen waje.
Shugaban kasar zai kashe makusan kudaden ne da mataimakinsa ta fannin abinci da walwalarsu da kuma wasu hidumomi na bukatunsu.
Kuma a cikin kudin ne za a riga lura da jiragen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke amfani dasu na gwamnati.
Manema labarai na PUNCH ne suka ruwaito wannan labarin, inda rahoton ya kara da cewa wadan nan kudaden na daga cikin kasafin kudi na shekarar 2023 da shugaba Buhari ya gabatarwa majalissar dattawa na naira triliyan 20.1.
Hakazalika
Gwamnatin tarayya zata biya kudin haya na miliyan 76 a Villa, kuma zata sha man janareta na miliyan 30
Gwamnatin tarayya zata biya kudin haya na miliyan 76 a Villa dake babban birnin tarayya Abuja.
Yayin da kuma gwamnatin tarayyar hallau zata sha man futur da janareta na naira miliyan 30.
A karshen wannan makon ne shugaban kasa Muhammdu Buhari ya gabatarwa majalissar dattawa kasafin kudi na shekarar 2023 na naira triliyan 20.1.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
