Connect with us

News

Yakin Ukraine da hauhawar farashin kayayyaki ya jefa yara miliyan hudu cikin talauci

Published

on

UNICEF
Advertisements
ads

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce yakin da ake a Ukraine da kuma karuwar hauhawar farashin kayayyaki a duniya ya jefa yara miliyan hudu da ke sassan gabashin Turai da tsakiyar Asiya cikin talauci.

Advertisement

Wani rahoto da Asusun ya wallafa a game da ranar yaki da talauci ta duniya, ya yi gargadin cewa hakan zai iya haifar da daina zuwan yara makaranta da kuma mace-macen kananan yara.

Kwankwaso ba zai halarci taron tattaunawa da ‘yan takarar shugabannin kasa ba

Wakiliyar BBC ta ce Rasha ce ke da alhakin fadawar kusan kashi uku cikin hudu na yaran da ke fama da matsananciyar yunwa.

Sannan kuma rabin yaran Ukraine na fama da talauci a wannan shekarar.

Babban daraktan asusun a yankin Afshan Khan, ya ce shiga kangin talauci ga yaran zai iya haifar da rasa rayuka da rashin ilimi da kuma rasa kyakkyawar rayuwa a gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending