News
Babban Bankin Najeriya Yana Da Goyon Bayana Wajen Sauya Takardun Kudi, Inji Shugaba Buhari.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce matakin da babban bankin Najeriya CBN ya dauka na sauya fasalin takardun Naira ya samu goyon bayansa kuma yana da yakinin cewa al’ummar kasar nan za su ci riba mai yawa ta yin hakan.
Da yake magana a hirar da yayi da gidan talabijin na Tambari TV, Shugaba Buhari ya ce dalilan da babban bankin ya shi sun tabbatar masa da cewa tattalin arzikin kasar nan zai ci gajiyar raguwa hauhawar farashin kaya, jabun kudin da kuma yawan kuɗaɗen da ke yawo.
Wata mata ta kashe mijinta da guba a Borno
Shugaba Buhari ya ce ko kadan wa’adin watanni uku na canjin sabbin takardun kudi bai yi kadan ba.
“Mutanen da ke da kudaden haram da aka binne a karkashin kasa za su fuskanci kalubale da wannan amma ma’aikata, da ƴan kasuwa da ke da kudaden shiga ba za su fuskanci matsala ba.”
A cikin hirar, shugaba Buhari ya kuma yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi samar da abinci da tsaron kasa da dai sauransu.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
