Connect with us

Business

Nijeriya da Mexico sun ƙulla yarjejeniyar kasuwancin zoɓo

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Ƙasashen Najeriya da Mexico sun saka hannu kan yarjejeniyar kasuwancin zoɓo a tsakaninsu.

 

Advertisement

Gidan talabijin na gwamnatin Najeriya NTA ya ruwaito cewa ƙasar ce kan gaba wajen shigar da ganyen zoɓo Mexico kafin su dakatar da kasuwancinsa a 2017.

Gwamnatin Yobe ta ba da mafi kyawun lambar yabo ta Jiha

Dr Vincent Isegbe, babban darkta a hukumar kula da dabbobi da tsirrai a Najeriya (NAQS), shi ne ya saka hannu a madadin Najeriya inda Dr Javier Arriaga ya wakilci Mexico a birnin Mexico City.

 

“Wannan yarjejeniya za ta ƙarfafa kasuwanci tsakanin Najeriya da Mexico,” a cewar Jakadan Najeriya a Mexico Rafiu Adejare.

 

Advertisement

Ya ƙara da cewa yanzu haka akwai ‘yan Mexico da ke gudanar da ayyukan noma a Jihar Gombe da ke arewacin Najeriya.

 

A 2017, hukumar NAQS ta bayyana cewa Najeriya na samun dala miliyan 35 daga kasuwancin zoɓo a faɗin duniya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending