News
Ƴar Nijeriya, Amanda Azubuike ta zama Birgediya-Janar a sojojin Amurka
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata soja ƴrar asalin Nijeriya, Amanda Azubuike ta samu karin girma daga Laftanar-Kanar zuwa Birgediya-Janar na Sojojin Amurka a wani sansanin soji da ke Fort Knox, Kentucky, Amurka.
Nijeriya da Mexico sun ƙulla yarjejeniyar kasuwancin zoɓo
Azubuike, haifaffiyar Landan kuma mahaifanta ƴan Nijeriya, ta shiga aikin sojan Amurka ne a shekarar 1994, inda ta zama jami’a a fannin jirgin sama bayan ta kammala kwas ɗin jirgin sama na Kwalejin koyon tukinn jirage ta sojoji.
A cikin sakon taya murna ta twitter, Manjo Janar Antonio Munera ya ce: “Ina taya murna ga sabuwar USACC da ta samu ci gaba @dcg_armyrotc, Brig. Janar Amanda Azubuike! A yau, ta karɓi tauraruwarta ta 1 daga Janar James Rainey, @armyfutures, yayin wani biki tare da dangi, abokai, da shugabannin al’umma.
Azubuike ta na aiki a matsayin Mataimakiyar Kwamanda a Rundunar Sojojin Amurka ta Cadet kuma a baya ta zama Babbar Hafsan Hafsoshi/Babban Mai Ba da Shawara kan Soja a Ofishin Sakataren Tsaro.
Ta kuma kasance Shugabar Hulda da Jama’a a Kudancin Amurka, yankin Fort Lauderdale, da Daraktar Hulda da Jama’a, Haɗin gwiwar Rundunar HQs-‘National Capital Region/Military District ta Washingtonc.
Ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara na Sadarwa don Ƙungiyar ‘Yan Wasan Kwallon Kafa ta Ƙasa da kuma ma’aikaciyar Hulɗa da Jama’a ta ƙungiyar NFL, Washington Redskins.
Azubuike ta na da digiri na farko na Kimiyya a harkar sadarwa da ilimin kafafen yaɗa labarai a Jami’ar Central Arkansas, Jagoran Fasaha a Tsaron Kasa da Nazarin Dabaru daga Kwalejin Yakin Sojan Amurka, kuma Jagora ce ta Nazarin Kwararru, Hulɗa da Jama’a / Sadarwar Kasuwanci daga Jami’ar Georgetown.
