Connect with us

News

Amurka za ta goyi bayan ƙasashen Afirka shiga ƙungiyar G20

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Amurka ta shirya tsaf don goyon bayan ƙungiyar Tarayyar Afirka a yunƙurinta na zama mamba a ƙungiyar ƙasashe 20 mafiya girman tattalin arziki ta G20, kamar yadda jaridar Washington Post ta ruwaito.

 

Advertisement

A mako mai zuwa ne Shugaban Amurka Joe Biden zai gana da shugabannin Afirka.

 

Advertisement

Afirka ta Kudu ce kaɗai ƙasar Afirka da ke cikin ƙungiyar ta G20.

INEC za ta sauya wa rumfunan zaɓe 357 waje a Katsina sabo da rashin tsaro

“Lokaci ya wuce na ƙasasen Afirka su samu kujerun zama a ƙungiyoyin duniya da sauran harkoki,” a cewar Judd Devermont, jami’i mai kula da harkokin Afirka a Fadar White House, cikin wata sanarwa.

Advertisement

 

“Akwai buƙatar ƙarin ƙasashen Afirka a harkokin ƙasashen duniya da suka shafi al’ummomi game da dimokuraɗiyya da tattalin arziki da shugabanci da sauyin yanayi da lafiya da tsaro.”

Advertisement

 

Shugabannin Afirka ta Kudu da Senegal sun matsa wa Shugaba Biden don ya goyi bayan wakilcin Afirka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending