Connect with us

News

Wata sabuwa farashin litar man fetur ta kai N310 a wasu gidajen mai a jihar Kano.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Dogayen layukan mai sun sake dawowa a gidajen mai a Kano, tun a karshen mako saboda karancin man fetur, wanda daidaikun gidajen mai ke sayarwa a halin yanzu.

Advertisement

Amurka za ta goyi bayan ƙasashen Afirka shiga ƙungiyar G20

A yayin da gidajen da mansu ya kare suke a rufe, wasu masu shi tuni suka kara farashi, inda wasunsu ke sayar da lita a kan N310 , wasu kuma sun rufe sun koma sayar wa masu bumburutu.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

A gidajen mai ’yan kalilan da ke da man kuma ba su kara farashin litar man fetur ta kai N310 ba

 

Advertisement

Tuni dai fasinjoji suka fara kokawa, a yayin da wasu masu ababen hawa daga garin Kano kan fita zuwa gidajen man da ke kan hanyan kauyuka su shan mai.

Wani mai tuka babur din A-Daidaita-Sahu, mal abba usman yace, ya shaida wa jaridar indaranka cewa ya shafe kimanin awa biyu a kan layi kafin ya samu mai.

Advertisement

 

“Har yanzu ba a kara farashi ba a gidajen man da na sha mai daga jiya zuwa yau (juma,a).

Advertisement

 

“Suna sayar da lita a kan N230 amma sai da na kai awa biyu kafin na samu, wanda hakan na shafar sana’armu, kuma fasinjojinmu ba za su fahimta ba idan aka yi musu karin kudi.”

Advertisement

 

Amma wasu masu ababen hawan sun ce sukan sha mai a cikin garin Kano, a kan sabon farashi da aka kara, kuma suka wuce minti 30 a kan layi.

Advertisement

“Jiya (juma,a) na sha mai amma lita a kan N310 , akan hanyar unguwa uku yan awaki kuma sai da na bi layi.

“Ban san me ya faru ba, amma na lura akwai karancin mai kuma an kara farashinsa,” in ji wani mai abin hawa, suleiman garba, a hirarsa da wakilinmu.

Advertisement

 

Kasuwar ’yan bumburutu ta bude

Advertisement

Wannan yanayi ya sa tuni kakar ’yan bumburutu ta yanke saka, inda suke kara N70 a kan farashin kowace lita daya ta man fetur.

Wasu daga cikinsu sun bayyana wa jaridar indaranka , “Mu ma sai mun bi layi a gidajen mai da tsakar dare muke samu, kuma sun yi mana karin kudi, saboda haka ba mu da zabi, dole sai mun kara farashi.”

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending