News
Jam’iyyar NRM Ta Yi Barazanar Kai Karar Bashir Ibrahim Rogo Kotu Kan Ikirarin Shi Ne Ɗan Takarar Gwamnan Kano
Jam’iyyar National Rescue Movement (NRM) reshen Jihar Kano ta yi barazanar ɗaukar matakin shari’a a kan Bashir Ibrahim Rogo idan har ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar.
Shugaban NRM na Jihar Kano, Alhaji Ado Muhammad Gama, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya jaddada cewa Bashir Ibrahim Rogo ba mamba ba ne a jam’iyyar, kuma ba ya cikin sahun mutanen da suka shiga harkokin jam’iyyar a hukumance.
KPCF Ta Yaba Wa Waiya Kan Inganta Hulɗar Gwamnati Da Jama’a A Kano
Gama ya ce jam’iyyar ba ta taɓa amincewa da Rogo a matsayin ɗan takarar gwamna ba, yana mai zargin cewa yana amfani da shafukan sada zumunta wajen yaɗa ikirarin da ba shi da tushe ko sahihancin doka.
Ya bayyana cewa ci gaba da amfani da sunan jam’iyyar ba tare da amincewarta ba na iya yaudarar jama’a tare da jefa martaba da kimar jam’iyyar cikin haɗari.
“Jam’iyyar NRM ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin shari’a idan Bashir Ibrahim Rogo ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar,” in ji shi.
Shugaban ya ƙara da cewa jam’iyyar ta riga ta kammala tantancewa da tsayar da ’yan takararta a dukkan muƙaman zaɓe a jihar, tun daga kujerar gwamna zuwa kujerun Majalisar Dokokin Jihar Kano, bisa tsarin jam’iyya da tanade-tanaden doka.
A cewarsa, dukkan ’yan takarar jam’iyyar sun samu tikitin takara ne bayan sun bi dukkan matakan da suka haɗa da tantancewa, zaɓen cikin gida da kuma amincewar hukumomin jam’iyyar.
Ya kuma jaddada cewa babu wani mutum da zai samu amincewar jam’iyyar a matsayin ɗan takara ba tare da bin sahihan matakan da kundin tsarin jam’iyyar ya tanada ba.
Gama ya yi kira ga mambobi da magoya bayan NRM a Kano da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda, tare da gujewa ɗaukar doka a hannunsu sakamakon wannan rikici.
Ya ce shugabancin jam’iyyar na ci gaba da jajircewa wajen gudanar da harkokin siyasa bisa doka, mutunta tsarin dimokuraɗiyya da kuma kare martabar jam’iyyar a kowane lokaci.
