News
An ɗaure ɗan siyasar adawa na Rasha shekara takwas a gidan yari
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An yanke wa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasar adawa a Rasha hukuncin shekara takwas da rabi a gidan yari.
An samu Ilya Yashin da laifin yaɗa abin da hukumomi suka kira labaran ƙarya game da yaƙin da Rashar ke yi a Ukraine.
INEC za ta sauya wa rumfunan zaɓe 357 waje a Katsina sabo da rashin tsaro
A watan Afrilu ne ya yi amfani da shafinsa na Youtube wajen tattauna batutuwan da suka tabbatar da irin ta’asar da sojojin Rasha suka yi a Bucha, kusa da Kyiv, babban birnin Ukraine.
Ya kuma bayyana shakku kan jawaban da hukumomin Rashar ke fitarwa game da yaƙin
Advertisements
