Connect with us

News

An yanke wa attajiri Jimmy Lai hukuncin daurin kusan shekaru 6 a gidan yari

Published

on

DAGA  KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

A yau Asabar aka sake yanke wa hamshakin attajirin Hong Kong, Jimmy Lai hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar da watanni tara bisa samunsa da laifin zamba.

 

Advertisement

Jimmy Lai wanda ya kafa jaridar Apple Daily, wata jarida mai sukar ikon kasar China da aka tilastawa rufewa,ya shafe watanni ashirin a gidan yari a baya-bayan nan saboda halartar zanga-zanga da tarukan da ba a yarda da su ba.

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar wa Gwamnan Ebonyi Umahi takarar sanata

Jimmy Lai na da shekaru 75, har yanzu za a yi masa shari’a nan ba da jimawa ba saboda hadin gwiwa da sojojin kasashen waje, wanda ya saba wa dokar tsaron kasa da China ta kafa wanda ke da hukuncin daurin rai da rai.

Advertisement

 

Yayin da zaman da ya yi a baya a gidan yari na da nasaba da rawar da ya taka a zanga-zangar neman dimokradiyyar shekara 2019.

Advertisement

 

Jimmy Lai da Wong Wai-keung, tsohon jami’in Apple Daily, an same su da laifin zamba a watan Oktoba.

Advertisement

 

A nasu bangaren, lauyoyin sun ce ya kamata a ce shari’ar ta kasance batun farar hula ne maimakon shari’ar laifuka, inda suka kara da cewa yankin da abin ya shafa ya yi kadan.

Advertisement

 

Mista Wong, mai shekaru 61, an yanke masa hukuncin daurin watanni 21 a gidan yari.

Advertisement

 

Alkalin ya soki jaridar Apple Daily da laifin cin mutuncin a matsayinsa na sanannen kafafen yada labarai don mayar da ita garkuwar kariya, wanda ya hana mai shi yin aiki idan aka saba ka’idojin yarjejeniyar.

Advertisement

 

 

Advertisement

FRI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending