News
MAKARANTAR AL’MADINA TAHAFIZUL QUR’AN DAWAKIN TOFA TA GUDANAR DA SAUKAR KARATUN AL’QUR’ANI MAI GIRMA
DAGA ISHAQ ISMA’IL DAWAKIN TOFA
Anyi kira ga daliban da su ji tsoron Allah (taqwa), su zamto masu kyawawan halaye da mu’amulla mai kyau tsakaninsu da al’umma, kuma su rika bibiyar Alkur’anin da suka haddace ko sauke, su girmama malamansu da kuma yi musu kyakkyawar addu’a akodayaushe
Shugaban kungiyar izalatul bidia, wa,igamatussunnah na karamar hukumar dawakin tofah malam Mustafa sani shine yayi wannan kira a lokacin da dalibai makarantar almadina tahafizuk kur,an dake dawakin tofa suke gudanar da farin cikin hadddace Al, Qur’ani Mai girma na makarantar.
Taran saukar ya guda,nane a ranar lahadi 25/12/2022. data gabata inda dalibai 90 suka hadddace Al Qur’ani Mai girma kamar yadda wakilin indaranka ya rawaito
Daliban sun karbi shaidar hadddace Al Qur’ani daga wakilin hakimin Dawakin Tofa kuma sarkin Dawaki mai tuta a masarautar Bichi Alhaji Kabiru Ali
Shugan malaman makarantar Malam Muhammad Auwal Bin Umar ya ce “an fara makarantar tun a shekara ta 1998 a unguwar Maratayi kana daga baya ta dawo cikin Model Primary duk a cikin garin Dawakin Tofa”.
A yayin taron dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Dawakin Tofa Honarabul Sale Ahmada Marke ta bakin wakilinsa kansilan mazabar Dawaki Gabas Honarabul Abdussalam Ishaq ‘Yarkanya bayan taya daliban murna, ya yi alkawarin baiwa kwamatin shirya taron saukar tallafin naira dubu hamsin da shadda yadi goma ga malamin da ya jogoranci dalibai darasu, sai atamfa turmi daya ga dalibar da ta karanta Alkur’ani tun a farko fara taron.
Malaman makarantar da dalibai da iyaye da alarammomi da limamai da kuma dandazon al’umma maza da mata ne suka shaida taron walimar kammala hadda da sauke littafin Alkur’ani mai girma, a harabar makarantar Model Primary dake kan titin zuwa makarantar Science ta Dawakin Tofa, a jihar Kano.
