Sports
Mutum 2 Sun Rasu Yayin Turereniya A Filin Kwallon Kafar Iraqi
DAGA YASIE SANI ABDULLAHI
Akalla mutum ɗaya ne ya rasa ransa sannan wasu 60 suka jikkata a wani turmutsitsi a wajen filin kwallon kafa da ke arewacin birnin Basra na ƙasar Iraqi.
Lamarin ya faru ne lokacin da dubban masoya kwallon kafa suka je filin wasa na Basra don kallon wasan karshe na gasar ƙasashen larabawa na yankin Gulf tsakanin Iraqi da Oman.
Gwamna jihar Yobe ya amince da rage Farashin Sabbin shaguna a sabuwar kasuwar zamani Da Ya Gina
Wani jami’in lafiya ya faɗa wa Kamfanin Dillancin Labaran Iraqi cewa sauran waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.
Hotunan bidiyo sun nuna mutane da dama kwance basa motsi a kasa.
Gasar kwallon kafar ta ƙasashen larabawa na yankin Gulf, shi ne gasar yanki na farko da aka gudanar a Iraqi sama da gomman shekaru.
An yi hakan ne domin dawo da kimar ƙasar bayan rikice-rikice na siyasa na tsawon shekaru
