Connect with us

News

Gwamnatin jihar Rivers ta wanke gwamna Nyesom Wike daga tsare mambobin yakin neman zaben Atiku Abubakar.

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

 

 

Gwamnatin jihar Rivers ta wanke gwamna Nyesom Wike daga tsare mambobin kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar.

Advertisement

 

 

Atiku Abubakar  shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP sun samu   takun saka da gwamnan Ribas bayan da ya kayar da shi  tikitin shugaban kasa jam’iyyar a bara.

Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan shari’ar Ahmad Lawan da Bashir Machina

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka samu rahotannin cewa wasu ‘yan sanda dauke da makamai sun kama  mambobin kungiyar 30 a wani taro a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

 

 

Advertisement

A cewar kakakin kungiyar yakin neman zaben Victor Moses, wasu daga cikin wadanda aka kama shugabannin kungiyar ne na jihohi da kananan hukumomi.

 

 

Ya yi zargin cewa jami’an ‘yan sandan na iya yin aiki da umarnin Gwamna Wike, wanda ya ki shiga ayyukan yakin neman zaben shugaban kasa na PDP.

 

Da yake mayar da martani kan zargin a ranar Litinin, kwamishinan yada labarai na jihar a jihar Ribas, Chris Finebone, ya ce rashin hankali ne kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar a jihar ta danganta gwamna Wike da duk wata matsala da za ta iya samu da ‘yan sanda.

Advertisement

 

Finebone ya shaidawa gidan Talabijin na Channels cewa zargin yana daya daga cikin abubuwan da mutane ke ganin ya dace su nuna yatsa ga gwamnatin da ke mulki.

 

Ko da yake kwamishinan bai tabbatar da kame ‘ya’yan kungiyar ba, amma ya ce idan mutane sun taka doka, dole ne jami’an tsaro su dauki matakin wanzar da zaman lafiya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending