News
An kori ‘yan sandan dake baiwa Mawaki Rarara tsaro daga aiki.
An kori jami’an ‘yan sandan dake baiwa mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, tsaro daga bakin aiki.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na kasa CSP Olumiyuwa Adejobi, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis.
‘Yan sandan da aka kora dai sune aka gani a wani bidiyo suna harba bindiga sama cikin nishadi lokacin da suke tare da mawakin a garin sa na Kahutu dake jihar Katsina yayin da yaje raba kayan abinci.
‘Yan sandan sun hada da Dahiru Shu’aibu mai mukamin Sufeto da Abdullahi Badamadi mai mukamin Sajan da Isah Dan Ladi shima mai mukamin Sajan.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
