Sports
Rundunar ‘Yan sandan Spain sun kama wadanda suka furta kalaman wariya ga Vinicius
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A wani sakon Twitter da suka wallafa, sun ce wadanda aka kaman shekarun su na tsakanin 18 zuwa 21.
Dan asalin kasar na Brazil ya fuskanci cin zarafi sosai musamman na nuna wariya a wannan kaka, domin a hukumanci a cikin kakar wasa biyu sau 9 ana shigar da korafin nunawa dan wasan wariya.
Gwamnatin Tinubu ce za ta kaddamar da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan—-Fashola
Bayan kammala wasan, dan wasan mai shekaru 22 ya soki gasar La liga inda ya ce ta masu nuna wariya ce, sai dai shugaban gasar Javier Tebas ya soki kalaman na Vinicius.
Amma a wani sakon da shugaban hukumar kwallon kafar Spain Luis Rubiales ya tabbatar da cewar gasar na fuskantar kalubale, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin.
Advertisements
