Labarai
Atiku Ya Caccaki Gwamnatin Najeriya Kan Rahoton Zabe Na Kungiyar Tarayyar Turai

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya kan yin watsi da rahoton da tawagar sa ido kan zabe ta kungiyar tarayyar turai ta fitar kan babban zaben da aka kammala na 2023.
Idan dai za a iya tunawa, babban jami’in sa-ido na Tarayyar Turai, Barry Andrews, ya yi ikirarin cewa kura-kuran da aka samu a zaben ya yi matukar illa ga amincin jama’a ga hukumar zabe ta kasa INEC.
SUDAN: Likitoci sun yi gargaɗi game da ƙaruwar cutar ƙyanda a Sudan
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar a karshen mako, gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton.
Da yake mayar da martani kan kalaman gwamnatin tarayya, mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban kasar kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya ce hukumar zaben ta kasa gaza wajen gudanar da ayyukanta a lokacin zaben kamar yadda kungiyar EU tayi zargi.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
