News
Shugaban Gwamnatin Kasar Jamus Zai Ziyarci Najeriya
Shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz zai ziyarci Najeriya a watan Oktoba a wani mataki na kara karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale, a wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, ya ce an cimma matsayar ne a gefen taron G-20 a birnin New Delhi na kasar India, inda shugaba Bola Tinubu da jagoran na Jamus suka gana.
Sanarwar ta ambato Scholz na yabawa da damar na ciyar da huldar tattalin arzikinsu gaba, yana mai cewa kasuwar Najeriya ta kasance wadda babu kamarta kuma kamfanonin Jamus na da tarihi a Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, bayan ganawa da jagoran na Jamus, Tinubu ya kuma tattauna da takwaransa na Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol wanda ya yabawa shugaban kan jagorancin yankin yammacin Afirka .
Wani labarin kuma An dakatar da Paul Pogba kan zargin shan kayan kara kuzari
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro