News
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Tir Da Yadda Gwamnatin Zamfara Ke Siyasantar da Harkar Tsaro.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Tarayya ta bayyana matuƙar damuwa kan wata sanarwa da ta fito daga Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal Dare.
Gwamnatin ta ce maimakon gwamnan ya nuna jin daɗi da farin ciki ganin yadda jami’an tsaro da hukumomin Gwamnatin Tarayya ke ta ƙoƙarin ganin an ceto ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau daga hannun ‘yan bindiga, sai ya maida matsalar siyasa don kawai ya cimma wani buri a siyasance.
An ci tarar makarantar da ta sa hotonan dalibanta a yanar gizo ba tare da izinin iyayensu ba.
Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Zargin Tattaunawa Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
Bukukuwan Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Ranar Haihuwar Fiyayyen Halitta.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka bayan ya nazarci yadda dokar ƙasa ta bai wa hukumomin Gwamnatin Tarayya ƙarfin ikon zabura domin ɗaukar matakan tabbatar da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, kamar irin yadda aka yi wa ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau.
A cewar sa, don hukumomin da aikin ceton ɗaliban ba su fito sun sanar da irin ayyukan ceto ɗaliban ba, hakan ba ya nufin ana wata ƙumbiya-ƙumbiya kamar yadda gwamnan Zamfara ya yi wa ƙoƙarin da ake yi karkatacciyar fahimta.
A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai a Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Suleiman Haruna, ya rattaba wa hannu, ministan ya bayyana cewa babu wani jami’in Gwamnatin Tarayya wanda ke tattaunawar sulhu da wani ko wasu gungun ‘yan bindiga.
Ya ce ita Gwamnatin Tarayya ta na nan kan matsayar ta ta tabbatar da bin duk wasu hanyoyin da su ka dace, waɗanda binsu zai tabbatar da an daƙile tashin hankula kuma an dawo da zaman lafiya a cikin jama’a.
Sai dai kuma ya ce, idan jama’ar wasu yankuna su ka yi tunanin ɗaukar irin matakan da wasu yankuna su ka ɗauka har su ka kashe fitilar tashe-tashen hankula, ta hanyar neman sasantawa, to Gwamnatin Tarayya ba za ta yi gaggawar taka masu burki ko yi wa shirin nasu Allah-wadai ba.
Idris ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomin ta na aiki haiƙan don kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da duk wasu ayyukan laifuffuka.
Daga ƙarshe, ministan ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta saurari shawarwarin dukkan masu wani tasiri domin ƙoƙarin samun hanyoyin da za a bi a kawo ƙarshen matsalolin tsaro