Connect with us

News

Jami’an NAPTIP Sun Kama Gidan Marayun Dake Siyar Da Yara Kanana

Published

on

Untitled design 2021 09 03T114124.225 (1)

Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa NAPTIP ta bayyana cewa jami’anta sun kama wani gidan marayu dake siyar da yara kanana a jihar Enugu.

‎A sanarwar da Hukumar ta yi a shafinta na Facebook dake yanar gizo ranar Laraba Hukumar ta ce ya ceto wasu yara kanana wadanda aka siyar a karyar cewa za a kula da su.

Advertisement

Jami’an ‘Yansanda Sun Cafke Wani Mai Safarar Makamai A Kano

‎Hukumar ta ce ma’aikatan ta sun kama wani Thaddeus mai shekara 51 wanda ya siyar da yaran wa wani kawunsa Elies.

Advertisement

‎”Yaran na tsare a ofishin mu domin duba lafiyar su.

‎Hakan da ya faru ya tada hankalin mutane musamman yadda ake cin zarafin yara kanana da sunan kulawa da su.

Advertisement

‎Hukumar ba ta fadu sunan gidan marayun ba da wurin da abin ya faru a jihar Enugu ba.

‎Ci Gaba da Gudanar da Bincike

Advertisement

‎NAPTIP ta tabbatar cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da abin dake faruwa a gidan marayun.

‎Hukumar ta yi kira ga mutane da su gaggauta kawo karan duk wanda suka ga yana cin zarafi ko safarar yara ga hukumar.

Advertisement

‎A Kudu maso Gabashin kasar nan mutane na yawan amfani da gidajen marayu a matsayin gidajen siyar da jarirai inda a wadannan gidajen wasu ke tsare ‘yan mata yi musu fyade domin ganin sun dauki ciki inda da zaran sun haihu a siyar da jariran.

‎Akan siyar da jarirai irin haka akan naira miliyan 1.5 zuwa biyu ya danganta da jinsin yaron.

Advertisement

‎Wani sakamakon binciken da wani cibiyar yada labarai ta gudanar ya bankado wani gidan marayun a jihar Anambra dake tilasta ‘yan mata suna haihuwa domin tabbatar da sun dauki ciki inda suna haihuwa a siyar da jaririn.

‎Binciken da cibiyar yada labaran ta gudanar ya nuna cewa siyar da jariran da ake yi a gidan marayun na samun goyan bayan wasu rikakiun ‘yan sanda da lauyoyi da alkalai.

Advertisement

‎A shekarar 2015 ne gwamnatin Najeriya ta fara amfani da dokar hana safarar mutane a kasar nan inda bisa ga dokar duk wanda aka kama za a daure shi ko ita a kurkuku na tsaron shekara 5 zuwa 10 tare da biyan taran naira miliyan daya.

‎Tun bayan fara amfani da dokan alkalai da dama sun yanke wa mutane da dama da aka kama da laifin safarar mutane a kasar nan.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending