News
Ƙalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
Masu ƙananan sana’o’i a Jihar Kano na ci gaba da kokawa kan yadda ƙarancin wutar lantarki ke janyo musu asara tare da kawo cikas ga ci gaban harkokinsu a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.
Binciken Jaridar Inda Ranka ya nuna cewa yawan katsewar wutar lantarki ya tilasta wa masu sana’o’i, musamman masu ɗinki, masu walda da masu sana’ar sanyi, komawa amfani da janareta da sola domin ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Sai dai, hauhawar farashin man fetur na ƙara jefa su cikin mawuyacin hali, inda yawancin su ke bayyana cewa kuɗin da suke kashewa wajen sayen fetur ya zarce ribar da suke samu.
Khadija Nasser, mai sana’ar ɗinki a Kano, ta bayyana cewa rashin ingantacciyar wuta na hana su gudanar da aiki yadda ya kamata. Ta ce, “Mun dogara da janareta saboda yawan katsewar wuta, amma tsadar fetur na cinye mana riba. Wani lokaci ma sai mun yi aiki ba tare da samun wani amfani ba.”
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa ƙananan sana’o’i su ne ginshiƙin samar da ayyukan yi da bunƙasar tattalin arziki, amma irin waɗannan ƙalubale na iya jefa su cikin durƙushewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba.
A faɗin ƙasar nan, matsalar wutar lantarki na ci gaba da zama babbar barazana ga ci gaban tattalin arziki, duk da dimbin kuɗaɗen da gwamnatoci suka zuba a fannin. Yawancin al’umma na ci gaba da koken rashin wadatacciyar wuta, lamarin da ke shafar harkokin yau da kullum.
