Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Sake Jaddada Aniyarta Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai Da Hukumomin Tsaro

Published

on

IMG 20260619 WA0003

Gwamnatin Jihar Kano ta sake nanata aniyarta ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya, kare dimokuraɗiyya da kuma inganta haɗin kan ƙasa.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin Taron Ƙasa Kan Tsaro da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta gudanarwa a Abuja.

Advertisement

‎Cin Hanci Ne Gidajen Da Shugaba Tinubu Ya Gina Wa Manyan Alkalai A Abuja ‎ ‎—Dr. Hakeem Baba

A cewarsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi imanin cewa kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma da kuma isar da manufofin gwamnati ga jama’a, musamman matasa.

Advertisement

Ya ce a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubalen yaɗuwar labaran ƙarya da bayanan da ke haifar da ruɗani, ya zama wajibi ga ‘yan jarida su ci gaba da taka rawar gani wajen tabbatar da gaskiya da ingantaccen bayani.

“Kafofin yaɗa labarai suna da nauyin sanar da jama’a ayyukan gwamnati tare da kare martaba da haɗin kan ƙasa. Wannan wani nauyi ne da ya rataya a wuyanmu a matsayin ‘yan ƙasa,” in ji Waiya.

Advertisement

Ya yabawa masu shirya taron kan zaɓen taken da ya mayar da hankali kan alaƙar da ke tsakanin tsaro da aikin jarida, yana mai cewa batu ne da ya dace da halin da ƙasar ke ciki a yanzu.

 

Advertisement

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamnatin Kano na ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar samar musu da kayan aiki da tallafin gudanar da ayyuka domin su samu damar sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata.

 

Advertisement

Ya ce tallafin ya shafi hukumomi daban-daban da suka haɗa da ‘yan sanda, NSCDC, JTF da sauran jami’an tsaro da ke aiki a jihar.

 

Advertisement

Haka kuma, Waiya ya tabbatar da cewa kafafen yaɗa labarai na gwamnati da masu zaman kansu a Kano na gudanar da ayyukansu cikin walwala ba tare da tsangwama ba, yana mai ƙara da cewa gwamnati na shirya horaswa lokaci-lokaci domin ƙara wa ‘yan jarida ƙwarewa da inganta aikin yada labarai.

 

Advertisement

Ya ce, “Muna ƙoƙarin gina kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da kafafen yaɗa labarai. Duk wani tallafi da muke bai wa jami’an tsaro, muna taimakawa ne wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”

A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da mutunta ‘yancin faɗar albarkacin baki da na kafafen yaɗa labarai, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki domin samar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending