Connect with us

News

KISAN ‘YAN NAJERIYA A AFIRKA TA KUDU: Oshiomhole Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kwace Lasisin DSTV Tare Da Kara Wa MTN Haraji ‎

Published

on

images (13)

Tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki tsauraran matakan tattalin arziki kan kamfanonin Afirka ta Kudu da ke gudanar da harkokinsu a Najeriya, domin nuna rashin amincewa da yadda ake cin zarafi da kuma kashe ‘yan Najeriya a kasar.

‎A wani faifan bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, Oshiomhole ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta kwace lasisin kamfanin DSTV, tare da kara wa kamfanin MTN haraji a matsayin martani ga hare-haren da ‘yan Najeriya ke fuskanta a Afirka ta Kudu.

Advertisement

Jam’iyyar PDP Ta Tsayar Da Mustapha Sule Lamido A Matsayin Ɗan Takarar Gwamna Jigawa A 2027

‎Ya ce, daukar irin wadannan matakai zai zama sako mai karfi ga gwamnatin Afirka ta Kudu, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta kare mutuncin ‘yan kasarta a duk inda suke.

Advertisement

‎“Ba za mu ci gaba da zura ido ana kashe ‘yan kasarmu ba tare da daukar mataki ba. Dole ne mu nuna cewa rayuwar dan Najeriya na da daraja,” in ji shi.

‎Oshiomhole ya kara da cewa irin wannan matsin lamba na tattalin arziki na iya tilasta wa shugabannin Afirka ta Kudu su sake nazari, su kuma nemi hanyar sulhu da gwamnatin Najeriya.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending