News
Jam’iyyar PDP Ta Tsayar Da Mustapha Sule Lamido A Matsayin Ɗan Takarar Gwamna Jigawa A 2027
Jam’iyyar PDP a Jihar Jigawa ta amince da Mustapha Sule Lamido, ɗan tsohon gwamna Sule Lamido, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ta hanyar masalaha a kakar zaɓen 2027.
An gabatar da ƙudirin amincewa da shi ne ta hannun Aminu Taura, tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha, yayin da Wada Abubakar Dokaji ya mara masa baya. An gudanar da tsarin ƙarƙashin jagorancin Shugaban PDP na Jihar, Babandi Ibrahim, inda aka tabbatar da shi ta hanyar jefa ƙuri’ar murya daga mambobin jam’iyyar.
Dakarun Sojin Sun Hallaka Jagororin ‘Yan Bindiga Anaruwa Da Gomina Da Wasu 7 A Zamfara
Mustapha Lamido, wanda shi ne ɗan takarar PDP a zaɓen gwamna na 2023, ya sha kaye a hannun gwamna mai ci, Umar Namadi na jam’iyyar APC, wanda ya samu ƙuri’u 618,449, yayin da Lamido ya samu 368,726. Ɗan takarar NNPP, Ibrahim Ringim, ya samu ƙuri’u 37,156.
Bayan amincewar, Lamido ya yi kira ga ‘yan jam’iyya da su ci gaba da haɗin kai tare da ƙarfafa jam’iyyar domin tunkarar zaɓen 2027.
