Connect with us

News

Dakarun Sojin Sun  Hallaka Jagororin ‘Yan Bindiga Anaruwa Da Gomina Da Wasu 7 A Zamfara

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Dakarun rundunar sojin Nijeriya, sun kashe wasu manyan jagororin ‘yan bindiga biyu—Anaruwa da Gomina—tare da wasu mutum bakwai a jerin hare-haren da aka gudanar cikin kwanaki uku a jihohin Zamfara da Katsina.

‎Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar, Sashe na 8 da Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.Ya bayyana cewa a Jihar Zamfara, dakaru daga sansanin gaba-gaba da ke Bagega sun kai wani farmaki mai haɗari a ƙaramar hukumar Anka, wanda ya kai ga kashe ‘yan ta’adda bakwai, ciki har da shahararrun jagorori Anaruwa da Gomina.

Advertisement

An Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Sabon Mataimakin Gwamna Kano

‎An kuma bayyana cewa Anaruwa ƙanin shahararren jagoran ‘yan bindiga ne, Kachalla Idi Aiki.

Advertisement

‎Laftanar Kanal Olaniyi ya ƙara da cewa a farkon farmakin, dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addan a kan hanyar Bagega zuwa Anka, inda aka yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ɓangarorin biyu.

 

Advertisement

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending