News
Ƴan sanda sun kama iyayen da suka yi wa yaransu auren wuri a kasar Indiya

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumomin kasar Indiya sun kama sama da mutane dubu daya a arewa maso gabashin kasar a ranar Talata a wani bangare na yaki da aurar da kananan yara a yankin a bana.
Tuni dai jihar Assam ta kame mutane 4,000 a wani yukuri da ta yi a watan Fabrairu, ciki har da iyayen yaran da suka yi aure da kuma ma’aikatan gwamnati wadanda suka yi rajistar auren kananan yara.
Alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa akwai kananan yara sama da miliyan 220 da suka yi aure a Indiya.
Duk da cewa al’amuran auren kanana yara sun ragu matuka a wannan karnin, har yanzu al’adar tana yaduwa.
A cewar Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), kalmar auren yara tana nufin duk wani aure ko kuma wani tsarin zama tsakanin yaro da bai kai shekara 18 da wani babba ko yaro.
Babban Ministan Jihar Himanta Biswa Sarma ya sanar da cewa, ‘yan sanda sun kaddamar da wani samame na musamman wanda aka fara tun da sanyin safiya.
Ya wallafa a dandalin sada zumunta na X (wanda aka fi sani da Twitter): cewa “Yawancin adadin wadanda ake tsare da su zai iya karuwa,” wanda a halin yanzu adadin ya kai 1,039.
