News
Jami’ar Sokoto ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari Makaranatar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar gudanarwar Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta jahar Sokoto ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a safiyar jiya Litinin.
Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Lawal Bilbis ya karyata wannan jita-jita , wanda wasu bata-gari ke yadawa da nufin haifar da rudani a Jami’ar.
Shigaba Tinubu Ya Nada Wanda Zai Maye Gurbin El-Rufa’i A Matsayin Minista
Farfesa Bilbis ya bayyana cewa, abin da ya faru shi ne kutsen da wasu ‘yan fashi da makami suka yi a kasuwar cikin Jami’ar wanda daga baya jami’an tsaro suka kama su.
Haka kuma “Tuni mun sanar da jami’an tsaro daban-daban a jihar kan bukatar kara sanya ido a cikin Jami’ar da kewaye.
“Harin ba na ‘yan bindiga bane kamar yadda ake hasashe a wasu sassan, a yi kira ga sauran jama’a da kuma iyaye da su kwantar da hankalinsu domin babu wani abin fargaba game da tsaron rayukan daliban Jami’ar”.
Mataimakin shugaban jami’ar ya kuma yabawa jami’an tsaro da kuma jami’an tsaro na cikin gida na makarantar bisa gaugawar daukar matakin da suka dauka kan lamarin.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
