News
Wata sabuwa farashin litar man fetur ta kai N650 a wasu gidajen mai a jihar Kano.

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
farashin Man fetur ya kai N.650 zuwa 640 akan Litre daya wasu Gidajen mai a jahar kano.
A yayin da gidajen da mansu ya kare suke a rufe, wasu masu shi tuni suka kara farashi, inda wasunsu ke sayar da lita a kan N650 zuwa 640.
Shigaba Tinubu Ya Nada Wanda Zai Maye Gurbin El-Rufa’i A Matsayin Minista
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa gidajen mai ’yan kalilan da ke da man kuma ba su kara farashin litar man fetur ta kai N620 ba
Tuni dai fasinjoji suka fara kokawa, a yayin da wasu masu ababen hawa daga garin Kano kan fita zuwa gidajen man da ke kan hanyan kauyuka su shan mai.
Wani labarin kuma Shigaba Tinubu Ya Nada Wanda Zai Maye Gurbin El-Rufa’i A Matsayin Minista
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
