Connect with us

News

Shigaba Tinubu Ya Nada Wanda Zai Maye Gurbin El-Rufa’i A Matsayin Minista 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Shugaban Koda Bola Ahamad Tinubu, ya aike wa Majalisar Dattawa sunan Balarabe Abbas Lawal a matsayin minista daga Jihar Kaduna.

Hakan na kunshe ta cikin wata wasika da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya karanta a yayin zamanta na ranar Talata.

Advertisement

Shehu Sani Ya Yabawa BUA Kan Rage Farashin Siminti, Ya Roki Masu Abinci Su Yi Koyi Da Shi

Tinubu ya kuma bukaci majalisar ta amince da nadin Dr Jamila Bio Ibrahim da Ayodele Olawande su ma a matsayin ministoci.

An dai nada Balarabe ne domin ya maye gurbin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda a baya majalisa ta ki amincewa da nadin shi tare da Sanata Abubakar Sani Danladi daga jihar Taraba da kuma Stella Okotete daga jihar Delta) saboda dalilai na tsaro.

Advertisement

Sai dai Tinubu ya bukaci majalisar ta amince da sabbin nade-naden da gaggawa.

Balarabe dai ya taba zama tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, kuma shugaban kwamitin karbar mulki na Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani a 2023.

Advertisement

Wani labarin kuma Shehu Sani Ya Yabawa BUA Kan Rage Farashin Siminti, Ya Roki Masu Abinci Su Yi Koyi Da Shi

 

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

Advertisement

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Advertisement

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending