Connect with us

News

Kanawa na zaman jiran hukuncin kotu kan zaɓen gwamnan jihar

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Al’ummar jihar Kano, musamman magoya bayan manyan jam’iyyun siyasa biyu na jihar APC da NNPP, sun wayi gari cike da zaƙuwa gabanin sanar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, da za a sanar nan da ‘yan sa’o’i cikin Juma’ar nan.

Hukuncin kotun, wadda ke zamanta a Abuja, yana da matuƙar muhimmanci ga siyasar jihar, mafi yawan jama’a da harkokin kasuwanci a arewacin Najeriya, kuma ginshiki ne ga makomar siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna, aƙalla tsawon shekara huɗu nan gaba.

Advertisement

Muhimmancin sada zumunci – Malam Jafar

Abba Kabir Yusuf ya garzaya gaban kotun ɗaukaka ƙara ne, bayan kotun ƙorafin zaɓe ta jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba, ta rushe nasarar da ya samu, inda ta ce abokin takararsa na jam’iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna ne halastaccen wanda ya ci zaɓe.

 

Advertisement

Kotun ta soke sama da 165,000 a cikin ƙuri’un Abba Kabir Yusuf na NNPP, bisa hujjar cewa ba su inganta ba, saboda rashin sa hannu da kwanan wata da kuma hatimin hukumar zaɓe.

 

Advertisement

Jam’iyyar APC ta roƙi kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Gwamna Abba Kabir.

 

Advertisement

Takara tsakanin ɓangarorin biyu, na ɗaya daga cikin mafi zafi da aka gani kafin zaɓen 18 ga watan Maris a Najeriya, kuma ga alama har yanzu, yanayin siyasar bai daina tafarfasa ba, wata takwas bayan kammala zaɓe.

 

Advertisement

Hukumomin tsaro a Kano, tun farkon wannan mako sun ce sun tura ƙarin jami’ai da kayan aiki zuwa manyan fuskokin garin, don hana faruwar tashin hankali, da kuma kare rayuka da dukiyar al’umma, tun kafin sanar da hukuncin.

 

Advertisement

Dukkan ‘yan takarar a zaɓen da ya wuce, suna da alaƙa da jiga-jigan ‘yan siyasar Kano biyu, Rabi’u Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje, tsoffin gwamnonin jihar da ke kan ganiyarsu har yanzu, sannan tsoffin manyan aminan juna, kafin su ɓaɓe a tafiyar siyasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending