News
Kotun Daukaka Kara ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Bauchi, ta Bada Umarnin Sake Sabon Zabe
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na tabbatar da zaben Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman, a matsayin memba mai wakiltar Ningi ta tsakiya, Tribune Online ta rahoto.
Bayan dai Kotun daukaka kara tayi watsi da Hukuncin kotun zabe ta ba da umarnin sake sabon zabe a rumfunan zabe goma.
Sai dai shugaban majalisar ya bukaci daukacin magoya bayansa da mazabarsa da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda, yana kallon lamarin a matsayin koma baya na wucin gadi da za a gyara nan ba da dadewa ba.
Shugaban majalisar ya bayyana amincewar sa da hukuncin da aka yanke, inda ya yi nuni da imaninsa a matsayinsa na musulmi a kan kaddara, duk da rashin alherin da aka samu.
Shugaban majalisar wanda ya bayyana hukuncin a matsayin karamin koma baya na siyasa, ba sabon abu ba a fagen siyasarsa, shugaban majalisar ya bayyana shirinsa na sake tsayawa zabe, da nufin kara tazarar kuri’u kusan dubu biyu da ya samu a baya a kan abokin hamayyarsa.
Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman ya jaddada cewa goyon baya da hadin kai da yake samu a garin Ningi har yanzu ba su gushe ba, inda ya yi watsi da duk wani yunkuri na kawo masa cikas.
Ya bayyana dalilin da ya sa aka tsawaita tsarin kada kuri’a daga ‘yan adawar sa, duba da sake zaben da za a yi a rumfunan zabe goma, wadanda su ne tungarsa, a matsayin takara kai tsaye.
Shugaban majalisar ya jaddada ci gaban da aka samu na samar da ababen more rayuwa da Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya kaddamar a karamar hukumar Ningi, inda ya tabbatar da matsayin da jam’iyyar PDP ta dauka a Ningi.
Ya yi alkawarin dagewa wajen isar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar mazabar Ningi ta tsakiya, ba tare da la’akari da yunkurin wasu abubuwa na kawo masa cikas ba.
Wadannan kalamai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abdul Ahmad Burra, Mai magana da yawun kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya fitar.
