Connect with us

News

Mai kallon fina-finan laifuka ta kashe mutum ‘don yi wa mutuwa ganin ƙwaƙwaf

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga wata mai kallon fina-finan laifuka, wadda ta faɗa wa ‘yan sanda cewa ta kashe wata mace ne “don ganin ƙwaƙwa”.

Jung Yoo-jung, ‘yar shekara 23, ta cika da saƙe-saƙen fina-finai da littattafan laifuka kuma ‘yan sanda sun ce jarrabawar da suka yi mata a kan lafiyar ƙwaƙwalwa ta tabbatar da lafiyarta ƙalau.

Advertisement

Sauke Abba Kabir daga mulki barazace ga rayuka da dukiyoyin Yarabawa mazauna Kano -Ƙungiyar Yarabawa

Damuwar da ta yi da tunanin “gwada aikata kisan kai”, sai ta yi amfani da wata manhaja don gamuwa da mai koyar da darasin Ingilishi, kuma ta caka mata wuƙa har sai da ta mutu a gidan malamar cikin watan Mayu.

Mugun kisan kan ya dugunzuma al’ummar Koriya ta Kudu.

Advertisement

Masu shigar da ƙara sun nemi a yanke mata hukuncin kisa – wata buƙata da akasari ake yanke wa mutanen da suka aikata laifuka mafi muni a ƙasar.

Sun faɗa wa kotu cewa Jung, matashiya ce maras aikin yi da ke fama da kaɗaici, wadda ke zaune a gidan kakanta, kuma ta shafe tsawon watanni tana neman mutumin da za ta hallaka.

Advertisement

Ta tuntubi sama da mutum 50 kuma ta riƙa fifita neman malama mace, inda ta riƙa tambayar ko malamar tana ba da darasi a cikin gidanta.

Bbc ta rawaito cewa A watan Mayu, ta bad-da-kama da sunan mahaifiyar wata ɗaliba mai karatu a babbar makaranta da ke buƙatar darussan Ingilishi, inda ta tuntubi malamar mai shekara 26, da ke zaune a kudu maso gabashin birnin Busan. ‘Yan sanda ba su bayar da sunan wadda aka halaka ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending