Connect with us

News

Hukumar NDLEA sun bankado wasu haramtattun kayyaki da ake yunkurin fitarwa zuwa kasashen Duniya

Published

on

Advertisements
ads

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun bankado wasu haramtattun kayyaki da ake yunkurin fitarwa zuwa kasashen Turai da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Asiya.

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya ce haramtattun abubuwan da aka kama sun hada da nau’o’in kwayoyi a cikin sabbin wando na jeans da kwalin sabulun gida da kwalayen abun sha.

Rundunar Soji Ta Kama Wasu Sojoji 3 Da Laifin Sata A Jihar Borno 

Da yake tabbatar da cewa an gudanar da aikin ne a Legas, ya ce daga cikin kayayyakin da aka kama sun hada da tramadol da aka boye a cikin sabbin wando na jeans da ke kan hanyar zuwa kasar Cyprus da kuma jigilar tabar wiwi da aka boye zuwa Dubai.

Wasu kuma na kan hanyar zuwa Hong Kong, da kuma jigilar wani haramtaccen abu da ya fito daga Florida a Amurka.

A wani labarin kuma Rundunar Soji Ta Kama Wasu Sojoji 3 Da Laifin Sata A Jihar Borno 

Advertisement

Yan sandan Kenya sun kama wata mata da ake zargi da jefa jaririyarta ƴar watanni takwas a cikin tekun Indiya ranar Lahadi.

 

Shaidu sun shaida wa kafafen yaɗa labaran kasar cewa, matar ta jefa jaririyar ne cikin teku daga wani jirgin ruwa a lokacin da ya doshi garin Mombasa da ke gaɓar teku.

Bidiyon yadda ake ceto jaririyar ya karaɗe shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa al’ummar Kenya da dama ke nuna ɓacin ransu ga matar da kuma jin dadin yadda aka ceto jinjirar.

“An garzaya da jaririyar don ba da agajin farko a cibiyar agaji ta Red Cross, inda aka kula da ita sannan aka sallame ta cikin yanayi mai kyau, an kuma kai mahaifiyarta ofishin ‘yan sanda domin yi mata tambayoyi.” kamar yadda kafafen yaɗa laarai na K24 da Citizen TV suka ruaito.

Tun farko ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce jariririyar tana cikin ƙoshin lafiya a cibiyarta ta agaji.

Advertisement

Har yanzu dai ba a bayyana ko irin tuhume-tuhumen da za a yi wa matar ba.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending