News
Barayin Waya Sun Kashe Dalibin Jami’ar Tafawa Balewa Dake Jihar Bauchi

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani dalibi mai karatun digiri a ajin 500 Level a fannin ilimin kasa a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, Joseph Agabaidu, ya mutu sakamakon wani yunkurin sata ta wayar tarho.
Jaridar DAILY POST ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a lokacin da yake komawa masaukin sa da ke Yelwa da ke wajen birnin Bauchi da misalin karfe 7 na yammacin ranar Asabar.
Hukumar NDLEA sun bankado wasu haramtattun kayyaki da ake yunkurin fitarwa zuwa kasashen Duniya
An ce marigayin shi ne babba a cikin ‘ya’yan gidansu da suke su hudu da suka je makaranta a ATBU da ke Bauchi.
Duk da kokarin ganin an taimaka masa da jinya, ya rasu a safiyar yau bayan jinyar da yayi akan raunukan da ya samu.
A halin da ake ciki, dalibai a ATBU na shirin gudanar da zanga-zangar lumana a yau litinin domin nuna shakku kan matsalolin tsaro tare da yin kira ga mahukunta da gwamnati da jami’an tsaro da su kara kaimi wajen kare lafiyar daliban.
Daya daga cikin daliban da ya yi magana a cikin kwarin gwiwa ya shaidawa DAILY POST cewa lamarin ya faru ne bayan wani abu makamancin haka da ya faru a watan Disambar da ya gabata da wani dalibin ATBU
A wani labarin kuma Hukumar NDLEA sun bankado wasu haramtattun kayyaki da ake yunkurin fitarwa zuwa kasashen Duniya
Wata zazzafar muhawara ta kaure a siyasar Najeriya kan kananan hukumomin da shugabanninsu ba zababbu ba ne, naɗi ne na gwamnonin jihohin kasar.
Lamarin ya biyo bayan ƙudurin da Majalisar Dattawan ƙasar ta amince da shi, na yin kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya riƙe kuɗin ƙananan hukumomin da ba su da zaɓaɓɓun shugabanni har sai an yi zabe.
A Najeriya dai an jima ana zargin wasu gwamnoni da shaƙe wuyan ƙananan hukumomin ƙasar, da kuma karkatar da kuɗaɗensu zuwa wasu ɓangarori na daban.
