Sports
An ci tarar JoseMourinho da Roma Yuro 40,000 saboda sukar alkalin wasa.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kocin Roma Jose Mourinho ya soki alkalin wasa Matteo Marcenaro kafin wasan Sassuolo da Roma inda ya nuna shakka kan nutsuwar alkalin wasan.
Kociyan kasar Portugal Jose Mourinho da kungiyarsa ta Roma sun cimma yarjejeniya da ofishin mai shigar da kara na hukumar kwallon kafa ta Italiya, inda kowannensu zai biya tarar Yuro 20,000 sakamakon zargin da kocin ya yi wa alkalan wasa a wasan da kungiyarsa ta buga da Sassuolo.
Hukumar INEC Za Ta Gudanar Da Zaɓukan Cike Gurbi A Watan Fabarairu
Ofishin mai gabatar da kara ya bude karar Mourinho bayan ya zargi babban alkalin wasa, Matteo Marcenaro, da kuma jami’in VAR, Marco di Bello, da “rashin nutsuwa” a “wasa mai irin wannan matakin”, wanda ya ce “kullum” yana kawo “mummunan sa’a” ga Romawa.
A taron manema labara, Mourinho yace sau 3 basu shi a matsayin alkalin wasa na hudu kuma yana ji cewa alkalin wasan ba shi da da nutsuwar da zai iya busa a wasa a irin wannan matakin.
Sannan ya kara da cewa: da ya bibiyi bayanan Marcenaroni, sai ya kasa samun kwanciyar hankali, hatta wanda zai kasance a VAR, alkalin wasa ne wanda a kodayaushe suke yin rashin sa’a a busar sa.
Sai dai Bayan cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin, an ci tarar Mourinho Yuro 20,000, inda da za a bai wa wata kungiyar da ke kula da masu cutar sankarau, Lymphoma da Myeloma (AIL), a ƙasar Italiya haka ita ma kuma Roma za ta biya wannan adadin kuɗin.
A wani labarin kuma Hukumar INEC Za Ta Gudanar Da Zaɓukan Cike Gurbi A Watan Fabarairu
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
