News
Babbar Magana: Zargin Fasto Bisa Ɗirkawa Wata Matashiya Ciki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.
Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Akwa Ibom sun kama wani Fasto Cocin Dutsen Zion Light House,Mai suna Solomon Ufot Ton bisa zarginsa da sace wata matashiya mai suna Okpo Eunice Kingsley Mai shekaru 16 da kuma laifin yi mata ciki.
Wiki time ta ruwaito cewa bayan ya ɗirkawa matashiyar ciki sai ya ɗauke ta zuwa wurin wani likitan ƙarya don a zubar da ciki wanda hakan ya yi sanadiyyar shanyewar ɓarin jikin ta.
Kwamishinan ƴan sandan, CP Olatoye Durosinmi, Shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar a yayin taron kwata na huɗu a hedikwatar rundunar da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Durosinmi ya ce: “A baya tun a shekarar 2021, bayanai sun nuna cewa wani Fasto mai suna Solomon Ufot Oton, Na cocin Dutsen Zion Light House, ƙauyen Oruko a karamar hukumar Urueoffiong Oruko ya sace wata Okpo Eunice Kingsley, yar shekara 16 da ke Titin Asawana ƙaramar hukumar Oron inda ya ajiye ta a gidansa na tsawon kwanaki uku .
“Wanda ake zargin ya yi mata barazanar kar ta sake ta bayyana wa iyayenta game da lamarin.
“Bayan faruwar lamarin sai Faston ya ɗauki matashiyar ya Kaita wurin wani Likitan bogi don a zubar da cikin, wanda hakan yayi sanadiyyar shanyewar ɓarin jikin ta inda daga nan aka kai ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Uyo don ci gaba da yi mata jinya.”Wanda ake zargin ya amsa laifinsa.”
A wani labarin kuma 2023: Shekarar fara tonon silili, fallasa da tereren madaƙolon satar kuɗaɗe a shekaru 8 na gwamnatin Buhari
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
