News
Hukumar NDLEA Sun Cafke Wata Matashiya Da Ke Safarar Alburusai Ga Ƴan Fashin Daji A Kan Hanyar Kano Zuwa Zaria,
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar da ke Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta kasa (NDLEA), sun yi nasarar kama wata matashiya mai suna Bilkisu Suleiman da ke yiwa ƴan bindiga safarar Alburusai.
Jami’an Hukumar ta NDLEA sun kama Bilkisu Suleiman ne da alburusai guda 249 ɓoye a cikin wata baƙar jakar a lokacin da ke tafiya akan hanyar Kano zuwa Zaria, kamar yadda jami’in yaɗa labarai na hukumar Femi Babafemi ya fitar a cikin wata sanarwa a yau Lahadi.
Sanarwar ta ce “Jami’an NDLEA da ke sintiri akan hanyar Zariya zuwa Kano sun kama Bilkisu ne a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu dauke da harsashi har guda 249 da ta ɓoye a cikin wata baƙar jaka”
“Bilkisu Suleiman tana kan hanyarta ne ta kai wa wani ɗan bindiga Alburusan da ke zaune a ƙauyen Kakumi da ke jihar Katsina.”
Sahara Reporters ta ruwaito cewa Mista Femi Babafemi ya ce tuni sun miƙa Bilkisu zuwa ga rundunar ƴan sandan jihar Kaduna domin ci gaba da bincike.
A wani labarin kuma Amarya Ta Tura A Kashe Wadda Mijinta Zai Aura Ta 3
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
