News
A yau shekaru biyu kenan da rasuwar fitaccen malamin hadisinnan sheikh Dr Ahmad Ibrahim Bamba
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Yau Shekaru 2 Da Rasuwar Shiekh Ahmad Ibrahim Bamba B.U.K. Ya Rasu Ya na Da Shekaru 80 A Duniya.
A Rana Mai Kamar Ta Yau Ga 7 Ga Watan Junairu 2022, Allah Yayiwa Shahararren Malamin Addinin Musulunci Ahmad Bamba Rasuwa.
Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.
Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya inda ya kwana ɗaya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
DR Ahmad ya kasance malamai ne Mai tarin ilimin hadith Wanda manyan malamai da dama a fadin duniya ke karatu a karkashin,sa
A fagen iyali kuwa malan ya mutu yanada mataye biyu tare da tayin ya,ya da jikoki
Daga cikin magadan da malan ya rasu ya bari akwai wadan da aka samu domin dorawa akan inda malan ya tsaya tare da kwatan,ta siffofin mahaifin su wajen daukaka addinin Allah
manyan malaman addini musulenci a bangarori daban daban da Kuma al,ummar musulmi suka sallaceshi
A madadin daukacin ma,aikatan jaridar indaranka mukewa malan addu,ar Allah ya jaddada rahama garshi yasa aljannar firdausice makoma
