Sports
AFCON 2023: Karon-battar da za mu yi da Najeriya za ta yi zafi sosai —Kociyan Afrika ta Kudu
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD
Mai horas da ‘yan wasan Afrika ta Kudu, Hugo Bruce, ya bayyana cewa za su yi ƙasaitaccen shirin da ba su taɓa yi ba a Gasar AFCON 2023, yayin da Bafana Bafana za ta kara da Super Eagles, a wasan kusa da na ƙarshe.
Afrika ta Kudu za ta fuskanci Najeriya a wasan kusa da na ƙarshe, bayan ta doke Cape a ranar Asabar.
Dole ne mu bi kadin abinda aka yi wa Jami’anmu —Hukumar KAROTA
Mai tsaron gidan Afrika ta Kudu, Ronwen Williams ne gwarzo a wasan, yayin da ya buge bugun fenariti huɗu.
Sun dai tashi wasan ba wanda ya yi galaba bayan mintina 120, inda aka buga fenariti 5:3.
Rabon da Bafana Bafana ta kai wasan kusa da na ƙarshe tun 2000, sai wannan karon.
Kociyan su ya shaida wa manema labarai bayan bayyana tashi daga wasan su da Cape Verde cewa wasan da za su kafsa da Najeriya zai zama daban da sauran wasannin da suka buga, saboda Najeriya na da ƙwararrun ‘yan wasa, irin su Lookman.
Premium Times ta ruwaito cewa ya yaba wa ‘yan wasan sa, da ya ce sun nuna bajinta a wasan su da Cape Verde, musamman mai tsaron gidan su wanda ya buge bugun fenariti har huɗu.