Connect with us

News

Jam’iyyun ADP, LP sun lashe kujerun Sanata da Ƴan Majalisu a Filato

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Jam’iyyun ADP, LP sun lashe kujerun Sanata da Ƴan Majalisu a Filato

An bayyana dan takarar jam’iyyar Labour Party, LP, Daniel Asama, a matsayin wanda ya lashe zaben ‘yan majalisar wakilai na tarayya na mazabar Jos ta Arewa/Bassa da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Advertisement

Kwalejin Koyar Da Aikin Shari’a Ta Kano Wato Legal Za ta fara karatun Digiri a kwasa-kwasai takwas (8).

Da yake bayyana sakamakon zaben, jami’in zaben Farfesa James Garba ya bayyana Asama a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 66,422 inda ya doke abokin hamayyarsa Mohammed Gwani na jam’iyyar Peoples Redemption Party wanda ya samu kuri’u 61,670.

A wani lamari makamancin haka, an bayyana dan takarar jam’iyyar Action Democratic Party, ADP, Prince Pam Mwadkon Dachungyang, a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na sanatan Filato ta Arewa.

Advertisement

Da yake bayyana sakamakon zaben, jami’in da ke bayyana sakamakon zaben ‘yan majalisar dattawa, Farfesa Nestor Chagok, wanda ya sanar da sakamakon zaben da sanyin safiyar ranar Litinin, ya ce Yarima Dachungyang na jam’iyyar ADP ya samu kuri’u 122,442 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Yakub Muhammad Safiu na NNPP, wadda ya samu kuri’u 53,980.

Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Christopher Musa Giwa, ya samu kuri’u 39,132, yayin da Barr. Gyang Zi na jam’iyyar LP ya samu kuri’u 33,243.

Advertisement

DAILY POST ta ruwaito cewa a karshen shekarar da ta gabata ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Musa Agah na PDP da Sanata Simon Mwadkon, tare da bayar da umarnin sake gudanar da zaben cikin kwanaki 90.

Haka kuma, INEC ta cire PDP daga ƙuri’ar zabe, saboda hukuncin da aka ambata a baya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending