News
Mazauna Minna Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Adawa Da Tsadar Rayuwa Tare Da Toshe Manyan Tituna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mazauna Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Litinin, sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a najeriya, tare da toshe manyan tituna a cikin birnin.
Rahotanni na nuni da cewa masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa suna rera wakokin zanga-zangar, yayin da jami’an tsaro ciki har da ‘yan sanda badu kulawa.
Jam’iyyun ADP, LP sun lashe kujerun Sanata da Ƴan Majalisu a Filato
Masu zanga-zangar sun ce tsadar kayan abinci da kuma rashin kokarin da gwamnati ke yi na kame lamarin ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukansu.
Mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba, a lokacin da yake jawabi ga masu zanga-zangar, ya ce gwamnati na sane da kuncin rayuwa da iyalai ke fuskanta a wannan lokaci.
Ya ce gwamnati na kokarin rage tsadar rayuwa da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur.
